![]() |
Watan Ramadan yanada falala mai yawa kuma masu tarin albarka, kadan daga cikinsu sune:
1.Allah subhanahu wata'ala ya saukarwa manzon Allah s.a.w littafin dayafi komai girma aduniya wato alqur'ani .
2.Allah s.w.a yana ninkawa bayinsa lada akan dukkan wata ibada dasukayi ko meye qaramcinta misali idan kayi salati 1 Allah zai saka mala'ikunsa suyima 10 amma kuma watan Ramadan Allah zai saka mala'ikunsa suyima 20 sakamakon falalar watan Ramadan.
3. Allah s.w.a yana saukarwa bayinsa da abubuwa guda 3 acikin watan Ramadan wayannan abubuwan sune Rahama,Gafara,Tsira.
4.Allah s.w.a yabamu dare Wanda yake dauke da cikakkiyar falala wadda take ibada cikin wannan Daren tafi ibadar wata dubu ( shekara 83 da kwana 22 ) ayayinda wannan Daren yanazuwane cikin darerai 10 na karshen watan Ramadan .
Dan haka yan'uwana mezai Hana mudage akan neman wannan falalar mukasance masu ambaton Allah akowane lokaci domin neman dacewa da rahamar Allah da jinkansa.







